Isa ga babban shafi

Kasashen Afirka za su fuskanci karancin abinci saboda Nijar - Bankin Duniya

Bankin Duniya ya yi hasashen fadawar Najeriya da wasu kasashen yankin Afrika ta Yamma cikn halin karancin abinci da kuma tsadarsa, sakamakon matsalolin da suka biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar.  

Wasu mata kenan da ke cinikayya a wata kasuwa da ke yankin Afirka
Wasu mata kenan da ke cinikayya a wata kasuwa da ke yankin Afirka © guardian
Talla

Bankin ya bayyana cewar a halin yanzu, mutane sama da miliyan 3 da dubu 300 ne suka shiga cikin halin rashin abincin, wanda idan ba a dauki matakai a cikin gaggawa ba,  wasu mutanen miliyan 7 za su fuskanci karancin abinci a yankin. 

Takunkuman da aka kakaba wa Nijar sun hana shigar da abinci daga Nijar ko kuma fitar da shi, lamarin da ya yi illa ga hatta wasu kasashe makotan kasar.

Baya ga juyin mulkin Nijar, kazalika akwai matsalolin tsaro da kuma matsin tattalin arziki da su ma ke taka rawa wajen samun karancin abinci a yankin Afrika ta Yamma kamar yadda masa suka bayyana.

Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken rahoton da Muhammad Kabir Yusuf ya hada kan wannan kalubale.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.