Isa ga babban shafi

'Yan Ghana na zanga-zangar neman tsige gwamnan babban bankin kasar

Dubban mutane ne suka fito kan tituna a Accra babban birnin kasar Ghana a ranar Talata, suna neman a tsige gwamnan babban bankin kasar saboda abin da suka kira rashin tafiyar da harkokin tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, daidai lokacin da take fama da matsalar bashi mafi muni a tarihi.

Yadda maasu zanga-zanga ke neman a samar da sauyi ga tattalin arzikin kasar Ghana.
Yadda maasu zanga-zanga ke neman a samar da sauyi ga tattalin arzikin kasar Ghana. REUTERS - RALPH TEDY EROL
Talla

Irin wannan zanga-zangar ta kwanaki da dama ta mamaye babban birnin kasar a watan jiya, inda ‘yan kasar suka nuna baccin rai dangane da tsadar rayuwa, rashin aikin yi da kuma wahalhalu da ke neman wuce gona da iri..

Masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa babban ofishin babban bankin karkashin kulawar 'yan sandan kwantar da tarzoma, inda kungiyoyin maasu fafutuka ke yin kira ga gwamnan bankin Ernest Addison da mataimakansa biyu da su yi murabus.

Da dama daga cikin masu zanga-zangar na sanye ne da tufafi masu dauke da launin ja da baki, da aka saba gani a wurin jana’iza.

"Muna son Addison ya sauka daga kujerarsa, saboda ya nuna mana cewa ba zai iya tafiyar da bankin Ghana ba," in ji Emmanuel Quarcoo, mai shekaru 29, wanda ba shi da aikin yi.

A watan Yulin 2022 kadai, babban bankin Ghana ya yi asarar cedi biliyan 60.8 kwatankwacin dala biliyan 5.3, wanda masana ke ganin abin da ya janyo hakan sake fasalin baashi ne da gwamnati ta yi.

Kasar Ghana mai arzikin zinari da mai da koko, ta kulla yarjejeniya da asusun lamuni na duniya IMF kan bashin dala biliyan 3, domin taimakawa wajen daidaita tattalin arzikinta.

Addison, wanda ya kasance a kan mukamin tun 2017 kuma, a watan Satumba ya fitar da sanarwar cewa za a samar da Shirin da zzai karawa kasar hanyoyin samar da kudaden shiga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.