Isa ga babban shafi

Dakarun Mali sun yi ikirarin kwato garin Anefis da ya jima a hannun 'yan ta'adda

Dakarun gwamnatin sojin Mali sun yi ikirarin kwato garin Anefis da ke matsayin wata alkaryar tsayawar matafiya da 'yan ta'adda suka yi ikirarin kwacewa.

Daya daga cikin dakarun sojin Mali
Daya daga cikin dakarun sojin Mali REUTERS/Benoit Tessier/File Photo
Talla

Wata sanarwar da sojojin suka fitar, ta ce dakarun sun kwace garin da ke yankin Kidal na arewacin kasar bayan fafatawa da 'yan ta'addar.

Almou Ag Mohammed mai magana yawun kwamitin da sojojin suka kafa don maido da tsarin tsaro a yankin arewacin kasar ya ce sojojin sun farwa 'yan ta'addar ne a garin na Anefis mai nisan mil 70 daga kudancin yankin Kidal.

Almou ya kuma kara da cewa sojojin kasar, sun sami wannan nasara ne da hadin gwiwar sojojin hayar Wagner na Russia.

Jawabin nasa ya kuma kunshi yadda sojojin ke kara zage damtse wajen tunkarar 'yan ta'adda da 'yan tawayen da suka kaddamar da yaki a kasar.

Bayanai sun nuna cewa garin na Anefis ya jima a hannun 'yan ta'adda, wadanda suka shafe shekaru fiye da 10 suna aiwatar da ta'adddanci a kasar ciki kuwa har da kwace iko da garuruwa.

Tun bayan juyin mulkin Mali ake ci gaba da ganin karuwar hare-haren ta'addanci, baya ga sake bullar kungiyar tawaye ta Abzinawa, abinda ake ganin watakila yana da alaka da ficewa sojojin Faransa da na majalisar dinkin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.