Isa ga babban shafi

Akalla mutane 23 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a Yaoundé

A kasar Kamaru ,akalla mutane 23 ne suka mutu sakamakon zaftarewar biyo bayan shatata ruwan sama da aka yi a yammacin jiya  Lahadi a birnin Yaoundé, babban birnin kasar ta Kamaru.

Zaftarewar kasa a birnin Yaounde
Zaftarewar kasa a birnin Yaounde REUTERS - STRINGER
Talla

Birnin na Yaounde na daga cikin yankunan da ake fuskantar rushewar gidaje jeyi-jeyi  a duk lokacin da aka tunkarin,ganin ta yada birnin yake zagaye da tsaunuka da gangara ba tare da an ayi aiki da tsari gina gidaje yada ta kamata.

Iftil’ain da ya faru a gundumar Mbankolo, da ke wajen arewa maso yammacin birnin Yaoundé, kuma ya faru ne sakamakon fashewar wata madatsar ruwa a wani tafki na wucin gadi  kmamar dai yada kafafen yada labaren kasar suka ruwaito.

Kasuwar Birnin Yaounde
Kasuwar Birnin Yaounde © AFP/Charly Triballeau

  A bangaren  hukumar kashe gobira ta kasa, Shugaban hukumar David Petatoa Poufong ya shaidawa manema labarai a safiyar yau litinin cewa ma’aikatan hukumar sun samu nasarar zakulo gawarwakin mutane  15 a jiya kuma da safiyar yau litinin sun gano wasu matatun 8.

Wani Jami’in kwana-kwana a wurin da al’amarin ya faru ya bayyana cewa daga cikin mutanen da suka rasa rayukan su akwai yaro daya.

Zaftarewar kasa biyo bayan ruwan sama
Zaftarewar kasa biyo bayan ruwan sama Sarah Tétaud / RFI

Jami’an tsaro na kokarin nisanta farraren daga ainihin wurin da zaizayar kasa ta afku tare da dasa  shingen tsaro.

Gani girman wannan barna kasasncewa ruwan sun kwashe duk wani abu da ke kan hanyarsu, Daouda Ousmanou, shugaban sashin II na Yaoundé inda Mbankolo yake, ya isar da kira ga jama’a na su yi hatara wajen gina gidaje.

Ruwan sama
Ruwan sama © RFI

A ranar 27 ga Nuwamba, 2022, akalla mutane 15 ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a wani yanki na tudu da ke gundumar Damascus, kudancin Mbankolo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.