Isa ga babban shafi

Kotu ta maida jagoran 'yan adawar Senegal cikin 'yan takarar shugaban kasa

Wata Kotu da ke birnin Ziguinchor na yankin Casamance, inda jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko ke da karfin magoya baya, ta ba da umarnin mayar da shi cikin jerin wadanda ke neman takarar kujerar shugabancin kasar.

Jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko.
Jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Alkalin kotun ya soke hukuncin haramta wa Sonko takarar ne da yammacin ranar Alhamis da ta gabata.

Hukuncin kotun ya zo ne a yayin da ake ci gaba da tsare fitaccen dan siyasar a wani asibiti da ke birnin Dakar, bayan yajin cin abinci na tsawon kwanaki 45 da yayi, matakin da ya dakatar a farkon watan Satumba saboda rashin lafiya.

Wannan ce dai nasara ta farko da Ousmane Sonko ya samu tun bayan sanya kafar wando guda da yayi da gwamnatin shugaba Macky Sall ta fuskar shari’a.

A karshen watan Yuli gwamnatin Senegal ta tuhumi jagoran 'yan adawar kasar Ousmane Sonko da aikata laifuka da dama, ciki har da tunzura da jama’a wajen tayar da bore da kuma zagon kasa ga fannin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.