Isa ga babban shafi

Kusan mutane miliyan 7 rikici ya raba da muhallansu a Congo - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce karuwar rikicin da ake samu a Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo, ya sanya mutane miliyan 6 da dubu dari 9 barin gidajensu, adadi mafi yawa a tarihin kasar da aka taba samu na ‘yan gudun hijira.

Wasu 'yan gudun hijirar  Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo a Arewacin Kivu.
Wasu 'yan gudun hijirar Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo a Arewacin Kivu. © badru Katumba / AFP
Talla

Rikicin da ake gwabzawa tsakanin mayakan M23 da kuma sojojin kasar a gabashin lardin Kivu, ya tsananta a watan Oktoban nan, musamman a gabashin birnin Goma.

Hukumar kula da ‘yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, yawancin mutanen da suka tsre daga gidajensu su ke makale a kan iyakar kasar na bukatar taimako.

Mayakan M23 da su ka yi kaka gida a gabashin kasar tun shekarar 2021, daya ce daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye a yankin, duk da kasan cewar sojojin kasashen duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Hukumar kula da 'yan cirani ta duniya ta ce a cikin wannan watan na Oktoba, kimanin ‘yan gudun hijira miliyan 5 da dubu dari 5 ne ke zaune a yankin gabashin Kivu da kudancin Kivu da Ituri da kuma Tanganyika.

Arewacin Kivu kadai, na da kimanin mutane miliyan daya da rikicin na M23 ya raba da muhallansu.

Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da wasu kasashen Yamma ciki harda Amurka da Faransa, sun zargi Rwanda da goyawa ‘yan tawayen Tutsi na M23 baya, zargin da tuni ta karyata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.