Isa ga babban shafi

Gwamnatin Guinea tace an sake kama Dadis Camara da ya tsere daga gidan yari

Afirka – Rundunar sojin kasar Guinea ta sanar da cewar dakarun ta sun sake kama tsohon shugaban kasa Moussa Dadis Camara da kuma mayar da shi gidan yari sa'oi bayan wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kubutar da shi daga inda ake tsare da shi.

Tsohon shugaban kasar Guinea Moussa Dadis Camara
Tsohon shugaban kasar Guinea Moussa Dadis Camara © LAMARANA DJEBOU SOW / AFPTV
Talla

Sanarwar da wani ministan kasar ya gabatar wanda lauyoyin tsohon shugaban suka tabbatar, tace an samu tsohon shugaban cikin koshin lafiya, kuma an sake mayar da shi gidan yari inda ake tsare da shi, ba tare da karin bayani akan yadda aka kama shi ba.

Lauyan shugaban Jocamey Haba ya tabbatar da mayar da wanda yake karewar gidan yari.

Ministan shari'ar kasar Alphonse Charles Wright ya bayyana cewar da misalin karfe 5 agogon GMT wasu mutane dauke da manyan makamai suka kutsa kai gidan yarin inda suka fice da mutane 4 da ake tsare da su, cikin su harda Kaftin Dadis Camara.

Wright yace hukumomin Guinea sun rufe iyakokin kasar, yayin da sojojin suka yi zargin cewar wani yunkuri ne na zagon kasa ga gwamnatin sojin.

Wata majiyar shari'a tace 'yan bindigan da suka kutsa kai gidan yarin sun ce sun je ne domin kubutar da Camara.

Wright yace bayan Camara an kuma kama Kanar Moussa Tiegboro Camara, daya daga cikin mutanen da 'yan bindigar suka kubutar daga gidan yarin.

Lauyan Tiegboro yace wanda yake karewa ya tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.

Kafofin yada labaran Guinea da dama sun bayyana cewar kai hari gidan yarin ba shi da nasaba da yunkurin juyin mulki, duk da jin karan harbe harbe a yankin Kaloum wanda ke dauke da fadar shugaban kasa da ofisoshin manyan jami'an gwamnati da shelkwatar sojin da kuma babban gidan yarin kasar.

Wata majiya daga tashar jiragen saman kasar tace babu wani jirgi da ya tashi yau asabar daga babbar tashar jiragen Conakry, saboda yadda ma'aikatan tashar jiragen suka kasa zuwa wurin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.