Isa ga babban shafi

Al'ummar Masar na kada kuri'a a babban zaben kasar

Al’ummar Masar na kada kuri’a a yau Lahadi, a daidai lokacin da yaki ke ci gaba da rinchabewa a Gaza da ke dab da iyakar kasar.

Zaben na bana na zuwa ne cikin kalubalen tattalin arziki
Zaben na bana na zuwa ne cikin kalubalen tattalin arziki REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Talla

Alamun farko-farko na nuna cewa shugaban kasar Abdel Fattah Al-sisi wanda ke takara a karo na uku zai sha daga kafin ya sake darewa Takara ko ma ya rasa damar sake jagorantar kasar a zaben mai cike da zazzafar adawa.

Karkashin mulkinsa, Al-sisi ya daure daruruwan mutane a gidan yari musamman ‘yan siyasa lamarin da ake ganin ka iya zane masa cikas, duk kuwa da cewa gwamnatin tasa ta yafewa daurarru sama da dubu daya, amma kungiyoyin kare hakkin dan adam na cewa an kama ninki hudu na adadin da aka saki.

Zaben na bana dai ya zowa masar ne a dai-dai lokacin da take fama da matsin tattalin arziki da tashin farashin kayayyaki da ya kai kaso 40 cikin 100, yayin da darajar kudin kasar ke kara faduwa kasa warwas.

Bayanai nan una cewa tun kafin matsalar tattalin arzikin, kaso 2 bisa uku na yawan jama’ar kasar miliyan 106 na rayuwa ne cikin talauci, ko kuma kasa da ma’aunin majalisar dinkin duniya.

Hukumar zabe ta kasar ta ce mutane miliyan 67 ne kadai ke da dama kada kuri’a kasancewar sune suke da katin zabe da hukumar ta tantance, sai dai kuma duk da haka akwai fargabar samun karancin fitar masu kada kuri’ar.

Ana sa ran kammala zaben ranar jibi Talata, sannan kuma a sanar da sakamako a ranar 18 ga watan da muke ciki na Disamba

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.