Isa ga babban shafi

Kenya ta fice daga kangin bashi bayan cire tallafi da sanya haraji- Ruto

A jawabin da ya gabatar yayin bikin zagayowar ranar ‘yanci da ya gudana a jiya Talata, shugaba William Ruto na Kenya, ya ce yanzu haka kasar ta fice kangin bashin da ya dabaibayeta yana mai jinjinawa manufofin tattalin arzikinsa da ya ce sunyi aiki matuka.

Shugaba William Ruto na Kenya a jawabinsa yayin bikin cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Birtaniya.
Shugaba William Ruto na Kenya a jawabinsa yayin bikin cikar kasar shekaru 60 da samun 'yancin kai daga Birtaniya. AP - Brian Inganga
Talla

Kenya mai yawan jama’a miliyan 53 da ke matsayin guda cikin kasashen Afrika mafiya karfin tattalin arziki wadda Birtaniya ta yiwa mulkin mallaka na gudanar da bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kan ne a dai dai lokacin da jama’a ke fusace kan tsadar rayuwa da hauhawar farashin da ake fama da shi.

Hauhawar farashin da Kenya ke gani na da nasaba da sabbin harajin da gwamnati ta sanya da kuma janye tallafi wanda ya jefa miliyoyin al’umma a matsin rayuwa.

Shugaba William Ruto a jawabinsa, ya ce wani lokacin sai an dauki mataki mai tsauri kuma mai radadi ga jama’a gabanin iya ceto kasa daga dabaibayin bashi da durkushewar tattalin arziki.

Duk da cewa shugaba Ruto bai bayyana ainahin adadin bashin da ake bin kasar a yanzu haka ba, amma y ace ma’aunin tattalin arzikin Kenya na GDP ya habaka da maki 5.4 cikin watanni 6 da suka gabata.

Tattalin arzikin Kenya ya gamu da mummunan koma baya ne tun lokacin annobar Covid kana yakin Ukraine ya sake yi masa illa kari kan farin da yankin kuryar gabashin Afrika ya yi fama da shi wanda ya kai ga karruwar bashin kasar baya ga durkusar da darajar takardar kudin shillings.

Zuwa watan Yunin da ya gabata dai, Kenya na da bashin yuro biliyan 64 da miliyan 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.