Isa ga babban shafi

Jami'an tsaron Senegal sun kama 'yan ci rani kusan 100 da ke shirin ketara teku

Jami’an tsaron Senegal na Jandarma, sun sanar da dakile yunkurin ‘yan ci rani kusan 100 na kokarin barin gabar ruwan kasar domin tsallaka teku don zuwa nahiyar Turai.

Wasu jami'an tsaron Senegal tare da 'yan kwana-kwana yayin kokarin rufe gawar wani dan ci rani da ya rasa ransa yayin kokarin tsallaka teku zuwa Turai, daga gabar ruwan garin Ouakam. 24 ga Yuli, 2023.
Wasu jami'an tsaron Senegal tare da 'yan kwana-kwana yayin kokarin rufe gawar wani dan ci rani da ya rasa ransa yayin kokarin tsallaka teku zuwa Turai, daga gabar ruwan garin Ouakam. 24 ga Yuli, 2023. © REUTERS/Ngouda Dione
Talla

An dai cafke ‘yan ci ranin 93 wadanda akasarinsu ‘yan kasar Mali ne a tsakanin ranakun Juma’a zuwa Asabar da suka gabata, a yankunan Thies da Saint-Louis.

Daruruwan ‘yan ci rani rukuni-rukuni daga wasu kasashen Afirka na ci gaba da hankoron ganin sun shiga nahiyar Turai, ta hanyar ketara teku mai cike da hatsari a kananan jiragen ruwa, duk da salwantar rayukan da dama daga cikinsu da ake samu, da kuma matakan hadin giwar kasa da kasa domin dakile kwarar bakin zuwa Turan daga Afirka.

Kididdigar da hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya IOM ta fitar a watan Satumban shekarar nan ta nuna cewar, ‘yan ci rani sama da 2,500 suka rasa rayukansu, yayin kokarin tsallaka tekun Mediraniya don shiga nahiyar Turai,  kwatancin kwacin karuwar adadin mutanen da suka mutu kenan da sama da kashi 60 cikin 100, idan aka kwatanta da shekarar bara ta 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.