Isa ga babban shafi

Sojojin Guinea na murkushe 'yan jarida

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta game da karuwar murkushewar da ake yi wa kafafen yada labarai a Guinea, tana mai kira ga gwamnatin sojin kasar da ta sauya taku nan take.

Shugaban mulkin sojin Guinea, Mamady Doumbouya tare da wasu mukarrabansa.
Shugaban mulkin sojin Guinea, Mamady Doumbouya tare da wasu mukarrabansa. AFP - JOHN WESSELS
Talla

Tun a cikin watan Mayun da ya gabata, murkushewar da ake yi wa kafafen yada labarai masu zaman kansu ta karu tare da katse hanyoyin sadarwar gidajen rediyo masu zaman kansu har ma da shafukan labarai na intanet, baya ga tsare ‘yan jarida da ake yi a kasar ta Guinea.

Shugaban Hukumar Kere Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya bayyana cewa, an ci mutuncin ‘yan jarida da razana su da kuma tsare su, yayin da aka kwace kayayyakin aikinsu da aka farfasa. Kazalika an katse hanyoyin sadarwar kafafen yada labarai.

Jami’in ya kara da cewa, an kuma toshe hanyoyin sadarwara dandalin sada zumunta da dama.

Jami’in ya ce, ya zama wajibi ga mahukuntan na Guinea da su gaggauta kawo karshen wannan cin zarafi tare da  dawo da ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma bayyana ra’ayoyi.

Guinea dai, na daya daga cikin kasashen Yammacin Afrika da aka bari a baya ta fuskar samun ci gaba a duniya duk kuwa da arzikin da take da shi na albarkatun karkashin kasa.

Tun a cikin watan Satumban 2021, sojoji ke jan ragamar kasar bayan sun yi juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.