Isa ga babban shafi

Nairar Najeriya ta shige sahun gaban kudade marasa daraja a duniya

Bayanai daga tarayyar Najeriya na cewa darajar naira ta yi faduwar da ba’a taba ganin irin ta ba tun shekarar 1999.

Naira na ci gaba da shan kaye a hannun dala a kasuwar 'yan canji
Naira na ci gaba da shan kaye a hannun dala a kasuwar 'yan canji AFP - PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Ta cikin wani dogon jawabi da kididdiga da mujallar tattalin arziki ta Bloomberg ta fitar ta ce shekaru kusan 25 kenan rabon da dala ta tumurmusa Nairar Najeriya irin haka a kasuwar chanji.

Mujallar bata tsaya iya nan ba sai da ta yi hasashen cewa darajar nairar zata ci gaba da faduwa kasar warwars a shekarar mai kamawa, matukar mahukunta basu yi gaggawar daukar mataki ba.

Bayanai na nuna cewa Nairar ta fadi da kaso 55 cikin dari a bana kadai, inda a jiya aka rika sayar da kowacce dalar Amurka daya tak kan naira 1,043, abinda ya sanya Nairar ta Najeriya matakin farko cikin kudi marasa daraja a Najeriya sai Fan na Lebanon da Peso na Argentina da ke biye mata baya.

Kididdigar mujallar ta ci gaba da cewa faduwar darajar Nairar ya fara ne tun lokacin da babban bankin kasar CBN ya bar kasuwa ta yi halinta a fannin sauyin kudade, kari akan haka kuma shugaba Tinubu ya cire talllafin man fetur.

Haka kuma mujallar ta ce a yanzu asusun kasashen waje na Najeriya na ganin tasku, kasancewa kullum kasa ya ke yi tun shekaru 6 da suka gabata, abinda ke da nasaba da wasu ka’idojin tattalin arziki da kasashen turai ke kakabawa Najeriya da sunan bayar da tallafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.