Isa ga babban shafi

An bayyana fargabar shiga cikin yanayin take hakkin dan adam a kasar Mali...

An shiga zaman fargaba, lura da yadda gwamnatin mulkin sojin Mali ke ci gaba da kamewa tare da garkame  malaman addini da ke sukar lamirinta, a gidajen yari.

Shugaban mulkin sojin kasar Mali  Colonel Assimi Goïta.na yi wa al'umar kasar jawabin karshen shekara ta ranar  31 desamba  2023
Shugaban mulkin sojin kasar Mali Colonel Assimi Goïta.na yi wa al'umar kasar jawabin karshen shekara ta ranar 31 desamba 2023 © ORTM
Talla

Bayan kama Sheikh Chouala Bayaya Haidara saboda sukar salón siyasar kasar a cikin watan jiya, a ranar alhamis da ta gabata ma an cafke wani malamin mai suna Bandiougou Traore, lamarin da masu fafutuka ke ganin cewa, babban koma-baya ne ga ‘yancin dan adam.

Ko a makon da ya gabata babban malamin nan, Imam Mohammed Dicko, ya bayyana fargabarsa bayan da mahukumtan mulkin sojin kasar ta Mali,  suka zargeshi da cin amanar kasa, sakamakon karba goron  gayyatar da mahukumtan kasar Aljeriya suka yi masa, domin tattauna samar damafita a tsakanin bangarorin dake rikici da juna a kasar ta Mali. Taron da ya ce, an gayyacesu su ma mahukumtan mulkin sojin,  amma suka ki halarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.