Isa ga babban shafi

Harin sama ya kashe sama da mutane 30 a Sudan

Bayanai daga Sudan na cewa an wayi gari ranar juma’a da rinchabewar yaki bayan lafawar da ya yi na wasu kwanaki da kuma yadda bangaren dakarun RSF suka shirya zama kan teburin sulhu.

Wasu wurare a birnin Khartoum da masu rikici da juna suka yi lugudan wuta
Wasu wurare a birnin Khartoum da masu rikici da juna suka yi lugudan wuta © Mohamed Nureldin Abdallah / RFI
Talla

Al’ummar birnin Khartoum sun tashi da hare-haren makamai masu linzami da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 33.

Watanni 9 kenan a jere ana tafka yaki a kasar ta Sudan tsakanin bangaren mataimakin shugaban kasar Mohammed Hamdan Daglo kuma jagoran RSF da kuma shugaban sojin kasar Abdul Fattah Al-Burhan.

Kididdiga ta nuna cewa yakin da ya ki ci yak i cinyewa ya yi sanadiyar hallaka mutane dubu 12,190 yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da miliyan 7 suka rasa muhallan su.

Ko a ranar Alhamis akalla fararen hula 23 aka hallaka a wasu hare haren da aka kai kudancin babban birnin kasar Khartoum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.