Isa ga babban shafi

Ambaliyar ruwa ta jefa mutane dubu 350 cikin bukatar agajin gaggawa a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ambaliyar ruwa mafi muni a cikin shekaru 60 ta yi sanadin jefa sama da mutaane dubu dari 3 da 50 cikin bukatar neman agajin gaggawa, inda yanzu haka ake iya kaiwa ga kauyuka da dama ta kwale-kwale ne kawai.

Wadanda ambaaliyar ruwa ta daidaita  a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Wadanda ambaaliyar ruwa ta daidaita a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. AFP - GUERCHOM NDEBO
Talla

Hukumar kula da agajin jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake ta kwararawa tun daga watan Oktoba ne ya haddasa tumbatsar kogin Congo, lamarin daya haddasa ambaliya.

Wannan lamari ya sa yanzu haka kimanin yara dubu 27 ne suka daina zuwa makaranta a yankuna da ambaliyar ta shafa.

A babban birnin kasar Kinshasha, wanda  ke da yawan al’umma kimanin miliyan 15, yankunan da ke da  gidajen jama’a da wuraren tarihi su na cikin ruwa tsamo-tsamo har yanzu.

Majalisar Dinkin Dunniya ta ce ana bukatar gudummawa daga kasashen duniya domin aiwatar da sshirin kasasfin dala miliyan 26 da ta yi don taimakawa da  abinci, kiwon lafiya da tsaftataccen ruwan sha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.