Isa ga babban shafi

Kamaru ta zama kasar farko da ta kaddamar da gangamin rigakafin cizon sauro

Yau Litinin Kamaru ta kaddamar da aikin gangamin rigakafin zazzabin cizon sauro, matakin da ya mayar da ita kasar farko da ta jagoranci wannan aiki a wani yunkuri na yakar cutar wadda sauro ke yadawa.

An dai gudanar da gwajin rigakafin a kasashen Ghana da Kenya gabanin Kamaru ta shige gaba wajen kaddamar da gangamin rigakafin.
An dai gudanar da gwajin rigakafin a kasashen Ghana da Kenya gabanin Kamaru ta shige gaba wajen kaddamar da gangamin rigakafin. AFP - BRIAN ONGORO
Talla

Gangamin na Kamar una zuwa ne vayan gwajin alluran rigakafin cutar a kasashen Ghana da Kenya, wanda masana suka tabbatar da tasirin rigakafin wajen iya kange yara daga kamuwa da cutar.

Bayan tababar kusan shekaru 40 wajen tantance sahihancin rigakafin cutar ta Malaria, WHO ta amince da allurer rigakafin na zazzabin cizon da za ta zama cikakkiyar kariya ga illar da cutar ke yi musamman a nahiyar Afrika.

Alkaluma sun nuna yadda cutar ta Malaria ko kuma zazzabin cizon sauro ke kisan yara ‘yan kasa da shekaru 5 kusan rabin miliyan duk shekara a Afrika  

A cewar hadakar Gavi da ke aikin samar da rigakafin cutuka, yanzu haka kasashe 19 ne za su fara amfana da rigakafin a shekarar nan kadai.

Akalla yara miliyan 6 da dubu 600 ake saran zu amfana da rigakafin zazzabin na cizon sauro cikin 2024 zuwa 2025 a kasashen da zuwa yanzu suka yi rijista don samun rigakafin.

Babban daraktan yaki da cutuka na hukumar dakile yaduwar cutuka ta Afrika CDC Mohammed Abdulaziz ya ce lokaci ne da hukumar ta jima ta na dako lura da muhimmancin rigakafin ga nahiyar wadda ta fi kowacce rasa rayuka sakamakon cutar ta Malaria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.