Isa ga babban shafi

Putin ya bayyana aniyar aiki tare da shugaba Mahamat Deby

CHADI – Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin yau ya karbi bakuncin shugaban Chadi, Mahamat Idriss Deby a birnin Moscow, a wani yunkuri na karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, a ci gaba da fadada huldar da kasar ke yi a nahiyar Afirka.

Russia's Putin hosting Chad's Deby today in Moscow
Shugaban Rasha Vladimir Putin lokacin da ya karbi bakoncin shugaban Chadi Mahamat Idris Deby via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Kasar Rasha na ta kokarin ganin ta dakile karfin fada ajin da Faransa ke da shi a yankin Afirka ta Yamma da kuma Sahel, ganin yadda take bunkasa dangantakarta da kasashen da Faransar ta yiwa mulkin mallaka sakamakon juyin mulkin da akayi ta samu tun daga shekarar 2020.

Mahamat Deby wanda ya karbi jagorancin Chadi tun daga shekarar 2021 bayan hallaka mahaifinsa yayin fafatawa da ‘yan tawaye, ya yi alkawarin shirya zabe a cikin watanni 18, amma daga bisani aka daga zuwa Oktobar wannan shekara.

A wani takaitaccen bayanin da aka nuna ta kafar talabijin, shugaba Putin yace kasar sa na fari ciki a kan yadda Deby ya tabbatar da zaman lafiya a cikin Chadi, inda ya kara da cewar zasu taimaka ma sa.

Wani rahotan da aka wallafa a shafin fadar shugaban kasar Rasha ta Kremlin, ta ruwaito shugaba Putin na cewa kasashen biyu na da damar bunkasa huldar dake tsakaninsu, yayin da Rashar zata ribanya guraban karatun da take bai wa daliban da suka fito daga Chadi.

Ziyarar Deby a Moscow na zuwa ne mako guda bayan ta Firaministan Jamhuriyar Nijar Mahamat lamine Zein, kasar da ke hulda kut-da-kut da Nijar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin bara, wajen hambarar da mulkin shugaba Bazoum Mohammed.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar da Burkina Faso sun juya baya ga Faransa da ta yiwa kasashen su mulkin mallaka, inda suka karkata akalar su zuwa Rashar.

Yanzu haka Rasha na da alaka sosai da wasu kasashen Afirka irin su Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tun bayan taimaka musu da sojojin hayar ta na Wagner suka yi wajen yaki da ‘yan ta’adda a karkashin jagorancin Yevgeny Prigozhin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.