Isa ga babban shafi

Senegal: an samu wata tarzoma a yayin da 'yan majalisar dokoki ke muhawara kan jinkirta zabe

'Yan majalisar dokokin Senegal sun yi muhawara kan wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba dangane da batun jinkirta zaben shugaban kasar da za a yi a wannan watan, wanda ya haifar da rikici a wajen majalisar dokokin kasar, lamarin da ya dauki hankulan kasashen duniya.

Dandazon masu zanga-zanga
Dandazon masu zanga-zanga © Premiumtimes
Talla

 

Jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa kananan gungun 'yan adawa a wajen zauren na majalisar dokokin kasar.

Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken "Macky Sall kama-karya" dangane da shugaban bayan da aka tarwatsa su.

Wannan takaddamar dai ta tashi ne a yankin da ba a saba ganin haka ba kasancewar yankin yayi suna wajen kwanciyar hankali a cikin garin Dakar, inda aka hada ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da manyan motoci a kokarin kare majalisar.

A yayin da Wani mai zanga-zangar Malick Diouf, mai shekaru 37, ya ce ba shi da wani dan takara da ya ke so kuma ba shi da katin zabe, amma yana ganin yana da matukar muhimmanci ya zo ya shiga zanga-zangar.

Shugabannin ‘yan adawa a kasar dai sun yi tir da wannan jinkirin da aka yi a matsayin wani juyin mulki, inda suka bayyana cewa wannan cin zarafi ne ga demokradiyya.

Mummunar zanga-zangar kan tituna ta girgiza Dakar babban birnin kasar, inda aka kama wasu 'yan takara biyu na 'yan adawa ciki har da tsohuwar Firaminista Aminata Toure, daga bisani aka sake su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.