Isa ga babban shafi

Kasashen Afrika renon Faransa na karkata hankalinsu kan China da Dubai

Alakar diflomasiyya da tattalin arziki da kuma tsaro tsakanin kasashen Afrika renon Faransa, na dada sukurkucewa biyo bayan dakushewar tasirinta a kasashen. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen ke kokarin kulla alakar tsaro da tattalin arziki da China da Turkiya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Amurka.

Shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdorahmane Tianni tare da Kanar Assimi Goita a Mali
Shugaban gwamnatin sojin Nijar Janar Abdorahmane Tianni tare da Kanar Assimi Goita a Mali © Niger Presidency
Talla

Kifar da gwamnatocin wasu kasashen yammacin Afrika na baya-bayan nan da suka hada da Nijar da Burkina Faso da Mali da kuma Guinea, wata 'yar manuniya ce ta dakushewar tasirin kasar Faransa a kasashen, wandanda mafiya yawa daga cikinsu tuni suka yanke duk wata alaka da ita.

 

Niagalé Bagayoko, kwararriya ce a fannin sasanta rikice-rikice a Afrika, ta ce yanzu haka wasu kasashen nahiyar suna sake fasalin dangantakarsu a kasashen waje domin cimma bukatun kasashensu maimakon kulla kawance tsakaninsu.

 

Wani masanin siyasar duniya kuma kwararre a Cibiyar Kula da Harkokin Kasa da Kasa da Tsaro ta Jamus, Wolfram Lacher, ya ce, kasashen Afirka da dama na neman sabbin abokan hulda a fannin tsaro, saboda abin da za su samu daga gare su ya sha bamban da abin da suke samu daga kasashe kamar Amurka da Faransa.

 

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali suna amfani ne da sojojin haya na Rasha, a wani yunkuri na kawo kaarshen hare-haren ta'addanci a yankunansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.