Isa ga babban shafi

'Yan gudun hijirar Sudan na cikin matsanancin hali a Chadi - NRC

Kungiyar da ke kula da ‘yan gudun hijiya ta kasar Norway, ta ce kimanin mutane dubu dari 7 da suka yi gudun hijirar daga Sudan zuwa gabashin Chadi, na cikin matsanancin yanayi, na rashin samun agajin da ya kama.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Sudan a sansanin Adré na kasar Chadi.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Sudan a sansanin Adré na kasar Chadi. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

A cewar sakateren kungiyar Jan Egeland da ya ziyarci wasu daga cikin sansanonin ‘yan gudun hijirar a Chadi, anyi watsi da ‘yan gudun hijirar wajen samar musu da ababen bukatu na yau da kullum, musamman kayan abinci da tsaftatatcen ruwan sha, lamarin da hukumomin bada agaji ke gargadin ka iya haifar da wata annoba.

Ya ce abubuwan da ‘yan gudun hijirar suka bayyana musu a zantawar da suka yi da su, ya tabbatar da irin halin kuncin da suke ciki.

Rahotanni sun nuna cewar, yawan mutanen da suka yi gudun hijira daga Sudan zuwa Chadi a cikin watanni 10 da aka yi a na rikici tsakanin sojojin kasar da kuma na RSF, ya fi gaba daya wadanda suka yi gudun hijira a lokacin rikicin Darfur na shekarar 2003.

Yadda wasu 'yan gudun hijirar Sudan ke kokarin samun ruwa a sansanin Adré, da ke Chadi.
Yadda wasu 'yan gudun hijirar Sudan ke kokarin samun ruwa a sansanin Adré, da ke Chadi. AFP - DENIS SASSOU GUEIPEUR

Ya ce a wancan lokacin manyan masu fada aji a duniya irinsu Bush da Tony Blair sun magantu kan lamari, sai dai a yanzu da bukatar da ake da ita ta zarce ta wancan lokacin, amma babu wanda ya maida hankali kan halin da ake ciki.

Rahotanni sun nuna cewa sama da ‘yan Sudan miliyan 10 da dubu dari 7 ne suka yi gudun hijira a wannan rikici, adadi mafi yawa da aka taba samu na ‘yan gudun hijira a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.