Gawarwaki sun fara rubewa a asibitocin barikinmu - Rundunar sojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta ce yanke wa barikokin sojin kasar wutar da kamfanin raraba wutar lanytarki na kasar ya yi, ya sa yanzu haka gwarwakin da ke dakunan ajiyar gawawwaki a asibitocin sojin sun fara rubewa.
Wallafawa ranar:
Babban hafsan sojin kasa na kasar, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja, ne ya bayyana haka a yayin wata ziyarar da ya kai wa ministan lantarki na kasar Adebayo Adelabu a Abuja.
Laftanal Janar Lagbaja, ya bukaci a taimaka wajen yafe kudin wuta daya kai naira biliyan 42 da ake bin barikokin sojin kasar.
Sai dai minitsan ya ce za a duba yiwuwar sake fasalin bashin da ake bin rundunar sojin, amma ba za a shafe shi ba.
Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki, da kuma hauhawar farashin kayayyaki da masana suka danganta da matsalar karyewar darajar kudin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu