Isa ga babban shafi

Katsina United da Kano Pillars zasu kara a wasan hamayya

Kungiyar kwallon kafa ta Katsina United a Najeriya zata karbi bakuncin sai masu gida wato Kano Pillars da yammacin yau a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke jihar Katsina.

Tambarin hukumar shirya gasar league din Najeriya
Tambarin hukumar shirya gasar league din Najeriya © NPFL
Talla

Wannan dai a iya cewa itace karawa mafi zafi da kungiyoyin biyu da ke arewa maso yammacin Najeriya zasu buga, a tsakiyar mako na 22 da fara gasar Premiyar Najeriya.

Mustapha Ibrahim dan wasan Kano Pillars shine ya ciwa Kano Pillars kwallo daya tilo da ta bata nasara kan Chanji Boys din na Katsina a wasan farko da suka kara dai-dai minti na 27 da taje wasa.

Dan haka wasan na yau mai zafi ne ga kungiyar Katsina United da ke neman nasara ko ta halin kaka, don rama kayen da ta sha a gidan Kano Pillars.

Chanji Boys din dai tana da makinta uku bayan nasara da ta samu kan Kwara United, sai dai kuma tana bukatar nasara a yau kan Kano Pillars wadda ta fita maki bayan  kwallo biyar da ta ratata a ragar Sunshine Stars a wasan da aka tashin ci 5-1.

Sauran wasanni da za’a buga a wannan mako sun hadar da karawar Lobi Stars da zata karbi bakuncin Sunshine Stars, sai Bayelsa United zata kara da Doma United, Remo Stars zata barje gumi da Enugu Rangers, yayin da Sporting Lagos zata kara da Akwa United bayan shan kaye hannun Gombe United da ci 2-0 a makon da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.