Isa ga babban shafi

An kashe jagoran 'yan adawar Chadi Yaya Dillo

Hukumomin kasar Chadi sun tabbatar da mutuwar daya daga cikin shugaban ‘yan adawa Yaya Dillo bayan wani samame da jami’an tsaro suka kai ofishin jam’iyyarsa a jiya, wanda ya jefa mazauna birnin Ndjamena cikin fargaba da tashin hankali.

 Yaya Dillo na da alaka ta jini da shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno
Yaya Dillo na da alaka ta jini da shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby Itno AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Mai gabatar da kara na gwamnatin Chadi Oumar Mahamat Kedelaye ya tabbatar da mutuwar shugaban ‘yan adawar a yau Alhamis, bayan artabun da akayi jiya.

Mutuwar Dillo na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta zargi jam'iyyarsa da kai wani mummunan hari kan hukumar tsaron kasar, lamarin da ya musanta shi kai tsaye a jiya.

Harin da aka kai kan hukumar tsaron ya zo ne bayan da aka kama wani ‘dan jam’iyyarsa ta PSF tare da zargin sa da yunkurin kisan shugaban kotun kolin kasar.

A jiya Laraba ne aka ji karar harbe-harbe a kusa da hedikwatar jam’iyyarsa da ke N'Djamena babban birnin kasar.

Wannan na zuwa ne kwana guda da gwamnatin Chadi ta sanar cewa, za a gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 6 ga watan Mayu, inda shugaba Mahamat da Dillo za su fafata da juna.

Mahamat dai ya dare kan karagar mulki ne bayan mutuwar mahaifinsa Idriss Deby Itno wanda ya rasa ransa a yayin fafatawa da 'yan tawaye a 2021, yayin da ya shafe kimanin shekaru 30 yana mulkar kasar kafin ajalinsa.

Har ya zuwa wannan lokaci mazauna babban birnin kasar na cikin fargaba dangane da abin da ka iya je ya komo, sakamakon arangamar ta jiya da kuma mutuwar shugaban ‘yan adawan.

Kasar Chadi tana ci gaba da fuskantar tashin hankali tun kafin mutuwar shugaba Idris Deby, wanda aka zargi ‘yan adawa da harbewa a fagen daga, yayin da dora ‘dan sa Mahamat Deby bisa karagar mulki ba tare da gudanar da zabe ba ya dada jefa kasar cikin rudani.

Taron kasar da aka gudanar dangane da makomar kasar ya nuna rashin amincewa da takarar Mahamat Deby, amma kuma sai ga shi jam’iyyar sa ta saka shi gaba domin zama mata ‘dan takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.