'Yan adawan Chadi sun zargi gwamnati da yi wa jagoransu kisan gilla
Babbar jam’iyyar adawa a Chadi ta zargi gwamnatin sojin kasar da kisan jagoranta a wani samame da dakarun kasar suka kai shelkwatarta gabanin zaben da ke tafe a watan Mayun wannan shekarar.
Wallafawa ranar:
Yaya Dillo Djerou shine babban abokin hamayya, kuma dan uwa ga shugaba Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya dare karagar mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar mahaifinsa.
Dillo ya mutu ne a ranar Laraba, bayan da sojoji suka yi wa shelkwatar jam’iyyarsa ta Socialist Party Without Borders a babban birnin kasar, N'Djamena, amma gwamnati ta musanta hannu a kisan nasa.
Wannan na zuwa ne bayan da jagororin mulkin sojin Chadi suka sanar da cewa za a gudanar da babban zaben kasar a ranar 6 ga watan Mayu.
Zaben zai kawo karshen shekaru 3 na gwamnatin rikon kwarya, da zummar maido da aiki da kundin tsarin mulki wajen jagorancin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu