Faransa ta ce dakarunta za su ci gaba da zama a Chadi
Gwamnatin Faransa ta ce dakarunta zasu ci gaba da zama a Chadi bayan da ta fice daga wasu kasashen yammacin Africa.
Wallafawa ranar:
Mali, Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso sun fatattaki Faransa daga kasashen su biyo bayan juyin mulkin da ya kawar da gwamantin fararen hula a kasar.
Akalla sojojin Faransa 1,000 yanzu haka ke zama a Chadi daya daga cikin kasashen da Faransa ta raina.
Da yake jawabi, wakilin shugaban Faransa Emmanuel Macron a Africa Jean-Marie Bockel ya ce babu wani dalili da zai sanya sojojin kasar su bar Chadi, kasancewar gwamnatin Faransa na da kyakyawar alaka da Chadi a halin yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu