Isa ga babban shafi

Gwamnatin Birtaniya ta dage kan shirin tura bakin haure kasar Rwanda

Majalisar dokokin Birtaniya ta tashi tsaye kan batun mayar da bakin haure zuwa kasar Rwanda,a jiya alhamis ne ‘yan majalisun kasar suka bukaci karin haske daga Firaministan kasar a wannan zance,duk kuwa da takaddamar da majalisar dokokin kasar ta yi kan shirin da ke cike da cece-kuce.

Bakin haure a kokarin tsalakawa zuwa yankin Turai
Bakin haure a kokarin tsalakawa zuwa yankin Turai © Borja Suarez/Reuters
Talla

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak ya bayar da bahasi a kai,da kuma tabbatar da tsarin na cewa a cikin watani masu zuwa kasar za ta mayar da yan cin rani da dama zuwa kasar Rwanda.

Firaministan na fatan sanya bakin hauren da ba bisa ka'ida ba a jirgi mai zuwa Kigali,tsarin da ake kyautata zaton zai taimaka don kawar da jam'iyyar adawa ta Labour a babban zaben da za a yi nan gaba a shekarar 2024.

Shirin na Firaminista Rishi Sunak ya fuskanci jinkiri a wani lokaci da ‘wakilai a babban zauren majalisar da ba a zaba ba, wato House of Lords, suka mayar da shi ga majalisar da nufin kawo gyara.

Ministan cikin gidan Birtaniya James Cleverly, yayin muhawara dangane da 'yan cin rani da za a dawo da su Rwanda
Ministan cikin gidan Birtaniya James Cleverly, yayin muhawara dangane da 'yan cin rani da za a dawo da su Rwanda AFP - MARIA UNGER

A farkon wannan makon ne,wakilan majalisar suka yi watsi da tarin gyaran da kudin ya kumsa,wandada suka bukaci a gudanar da binciken farko na wanan kudiri.

Firaministan Birtaniya Rishi Sunak
Firaministan Birtaniya Rishi Sunak © Kirsty Wigglesworth / AP

Mai Magana da yahun Firaministan Birtaniya ya ce abin takaici ne yadda wakilan majalisa suka mayar da wannan kudiri ga Majalisar ba tare da amincewa da shi ba.

A shekara da ta gabata,an fuskanci tsaiko tsakanin gwamnatin Birtaniya da Majalisa,al’amarin da ya sa Firaminista Sunak ya gabatar da dokar ta-baci a karshen shekarar bayan da kotun kolin Birtaniya ta yanke hukuncin cewa tura masu neman mafaka zuwa Kigali na kasar ta Rwanda ya sabawa dokar kasa da kasa.

Wasu daga cikin 'yan cin rani
Wasu daga cikin 'yan cin rani © www.newtimes.co.rw

Shawarar korar dai ta kasance mai cike da cece-kuce da kuma kalubalen shari'a tun bayan da tsohon Firaministan kasar Boris Johnson ya gabatar da ita a shekarar 2022. Duk da haka har yanzu ba a aika da bakin haure zuwa Rwanda ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.