Isa ga babban shafi

Mutane 50 sun ɓace sakamakon zaftarewar kasa a Jamhuriyar Dimokaraɗiyar Congo

Akalla mutane 12 sun rasa rayukansu, yayin da wasu fiye da 50 suka ɓace, biyo bayan iftila’in zaftarewar kasar da ya rutsa da su a Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo.

Yadda kasa ta zaftare a Jamhuriyar dimokaradiyar congo sakamakon Mamakon ruwan sama
Yadda kasa ta zaftare a Jamhuriyar dimokaradiyar congo sakamakon Mamakon ruwan sama REUTERS - STRINGER
Talla

Iftila'in zaftarewar kasar ya auku ne ranar Asabar a yankin kudu maso yammacin ƙasar.

Wani jami’in gwamnatin garin Dibaya Lubwe, da ke lardin Kwilu, inda lamarin ya auku, ya ce saukar ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ne ya haddasa zaftarewar ƙasar mai fadin gaske, wadda ta faɗa cikin kogin Kasai.

Lamarin dai ya auku ne a daidai lokacin da wani ƙaramin jirgin ruwa ya isa gaɓar kogin, yayin da kuma wasu mutane ke wankin kayansu daga gefe kaɗan.

Tuni dai mahukuntan a ƙasar suka tabbatar da aukuwar iftila’in da ƙasar ta shafe tsawon lokaci ba ta fuskancin makamancinsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.