Isa ga babban shafi

Bankin Duniya na shirin samarwa 'yan Afirka miliyan 300 lantarki

Bankin Duniya ya sanar da cewa, akwai shirin samar da lantarki ga mutanen Afirka akalla miliyan 300 da zai samar, amma tare da hadin gwiwar bankin raya kasashen Afirka nan da shekarar 2030.

Masana na ganin shirin zai taimaka wajen inganta rayuwar al'ummar nahiyar.
Masana na ganin shirin zai taimaka wajen inganta rayuwar al'ummar nahiyar. © reuters
Talla

A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya ce zai yi kokarin samarwa mutane miliyan 250 da wutar lantarki ta hanyar samar da makamashin da baya gurbata muhalli, yayin da bankin na Afirka zai tallafawa karin mutane miliyan 50.

Bankin ya lura cewa samar da lantarki wani muhimmin aiki ga ci gaban rayuwar dan adam da kuma bunkasa tattalin arziki.

Rahotanni na cewa, a halin da ake ciki al’ummar Afirka miliyan 600 ne basu da wutar lantarki, abin da ke haifar da koma baya ga sha’anin kiwon lafiya, ilimi, ayyukan yi, da kuma harkokin kimiyya da fasaha.

A cewar sanarwar, shirin hadin gwiwar zai taimaka sosai wajen kawo karshen manyan kalubalen da nahiyar Afirka ke fuskanta.

Bugu da kari, bankin ya ce dole ne gwamnatoci su samar da tsare-tsaren da za su jawo hankulan masu zuba jari ta yadda za a iya inganta hanyoyin samar da makamashin da baya gurbata muhalli, musamman ga nahiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.