Isa ga babban shafi

Ya kamata a yi gaggawar ceto rayuwar kananan yara a Mali - Save the Children

Kungiyar agaji da ke bai wa yara kariya ‘Save the Children’ ta ce ƙawanyar da mayaƙan ‘yan ta’adda suka yi wa garin Menaka a Mali, ya rutsa da mutane kimanin dubu 140, cikinsu har da ƙanan yara akalla dubu 80.

Aisha kenan diya ga Fouma da aka bawa gado a asibiti sakamakon cutar yunwa da ta ke fama da ita, a wani asibiti da ke Basaso.
Aisha kenan diya ga Fouma da aka bawa gado a asibiti sakamakon cutar yunwa da ta ke fama da ita, a wani asibiti da ke Basaso. Rachel Palmer
Talla

Tuni dai ƙofar ragon da ‘yan ta’addan suka yi wa garin na Menaka ya jefa dubun dubatar ƙananan yaran cikin tashin hankali, inda suke fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki, da kuma ɓarkewar cutuka.

Ƙawanyar da ‘yan ta’adda suka shafe watanni huɗu suna yi wa Menaka dai iri guda ce da ƙamshin mutuwar da mayakan suka fara yi wa birnin Timbuktu tun daga watan Agustan shekarar bara, wanda kuma har yanzu basu janye ba, koda yake lokaci zuwa lokaci akan shigar da kayayyakin agaji zuwa birnin.

A halin yanzu dai karancin muhimman kayayyakin masarufi da magunguna yayi tsanani ga al’ummar Menaka, birnin da ke karɓar baƙuncin ‘yan gudun hijira akalla dubu 33 da 600, waɗanda suka tserewa hare-haren ta’addanci a wasu sassan kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.