Isa ga babban shafi

Mutane 9 sun mutu a harin da aka kai sansanin ƴan gudun hijira a gabashin Congo

Aƙalla mutanne 9, cikinsu yara ƙanana 7 ne aka kashe a wani harin bam da aka kai sansanin ƴan gudun hijira a birnin  Goma na gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a jiya Juma’a, kamar yadda kakakin sojin ƙasar da ma mahukuntan yankin suka tabbatar jim kaɗan bayan aukuwar lamarin.

Wani sansanin ƴan gudun hijira a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Wani sansanin ƴan gudun hijira a birnin Goma na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. AFP - GUERCHOM NDEBO
Talla

Babu  wani ƙarin bayani a game da irin bam ɗin da aka yi amfani da shi wajen kai harin, ko kuma wadanda ke da alhakin kai harin .

Hare-haren da ƙungiyar ƴan tawayen M23 mai samun goyon bayan Rwanda  kai kaddamarwa tsawon shekaru 2 kenan yanzu ya fara karasawa birnin Goma a cikin ƴan watannin nan, lamarin da ya sa dubban mutane neman mafaka a  cikin birnin.

Fadar gwamnatin Jamhuriyar Dinomakardiyar Congo ta bayyana a wata sanarwa cewa shugaba Felix Tshisekedi ya katse rangadin da ya ke yi  a ƙasashen waje, inda ya yanke shawara dawowa gida a cikin ƙarshen mako.

Ba wannan ne karon farko da  da ake kai hari kan sansanin ƴan gudun hijira a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, ko a cikin watn Yulin shekarar da ta gabata, sai da wasu mayaƙa suka kai hari kan wani sansanin ƴan gudun hijira a gabashin ƙasar.

Gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, na fama da kungiyoyi da dama masu dauke da makamai, tun bayan da rikici ya barke a kasar a shekarun 1990, inda yanzu haka masu bincike suka ce akwai irin wadannan ƙungiyoyi sama da 100 a yankin da rikici ke ci gaba da ƙamari.

Ƙasar ta jamhuriyyar demokradiyyar Congo ce ta fi kowacce yawan ‘ƴan gudun hijira a Afirka, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa akalla mutane miliyan 5.6 ne suka kaurace wa gidajensu zuwa kasar sakamakon fadace-fadace. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.