Isa ga babban shafi

Za a yi zaɓen shugaban ƙasa a Chadi karon farko bayan mutuwar Idriss Deby

A gobe Litinin al’ummar Chadi za su kada kuri’a a zaɓen shugaban kasa a karon farkon tun bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar, Idriss Deby Itno, wanda ya mulki ƙasar tsawon shekaru 30.

Tsohon shugaban Chadi, marigayi Idriss Déby Itno.
Tsohon shugaban Chadi, marigayi Idriss Déby Itno. AP - Andrew Harnik
Talla

Rahotanni sun ce alamu na nuna cewa al’ummar kasar sun ƙagara  wannan rana ta zo, duba da yadda wasu mazauna Ndjamena, babban birnin ƙasar ke shaida wa manema labarai cewa a shirye suke su sanya ƙafar wanda guda da masu rike da madafun ikon ƙasar na yanzu.

Hukumar zaɓen ƙasar dai ta haramta ɗaukar hotunan sakamako ko kuma wallafa su a dandalin sada zumunta, ko ma  gidajen radio da talabijin.

Hasashe na nuni da cewa shugaba mai ci, Mahamat Deby Itno ne zai yi nasara a wannan zabe, duba da yadda  gwamnatinsa ta murkushe tasirin ƴan adawa.

Chadi ce ƙasa ta ƙarshe a yankin Sahel da ke da alaƙa da dakarun Faransa a halin da ake ciki, bayan da makwaftanta, Mali, Nijar da Burkina Faso, waɗanda ke ƙarkashin mulkin soji suka sallami Faransa da sauran manyan ƙasashen yamma daga ƙasashensu.

Yanzu masu sharhi sun yi itifakin cewa, abin da ke gaban ƙasashen yamma a game da Chadi yanzu shine tabbatar da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da jaddada matsayinsu a cikin ta, a daidai lokacin da Rasha ke neman gindin zama a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.