Isa ga babban shafi

Hatsarin jirgin sama ya jikkata mutum 11 a Senegal

Wani jirgin sama samfurin 737 dauke da mutane 85 ya tsallake rijiya da baya a filin tashi da saukar jiragen sama na Dakar, da ke kasar Senegal, inda ya raunata mutane 10, kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar

Jirgin TransAir da ya samu hatsari a Senegal kenan.
Jirgin TransAir da ya samu hatsari a Senegal kenan. © reuters
Talla

Mawakin kasar mai suna, Mali Cheick Siriman Sissoko wanda ya wallafa yadda lamarin ya auku a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa, "Jirgin da muke ciki kawai ya kama da wuta," yana mai cewa kururuwar mutane ta cika cikin jirgin a lokacin da al’amarin ya faru.

Ministan Sufuri El Malick Ndiaye ya ce jirgin Air Senegal ya nufi Bamako babban birnin kasar Mali da ke makwabtaka da kasar da yammacin Laraba, dauke  fasinjoji 79 sai kuma matukan jirgi biyu da ma'aikatansa guda hudu.

Wadanda suka jikkata dai suna karbar kulawar likitoci a asibiti yanzu haka, yayin da sauran kuma aka kai su otel domin su huta.

Har yanzu dai babu wani cikakken bayani kan musababbin faruwar hatsarin jirgin.

Cibiyar Safety Network mai bin diddigin hadurran jiragen sama, ta wallafa hotunan yadda jirgin ya kafe a cikin wani fili mai dauke da ciyawa a shafinta na X.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.