Isa ga babban shafi

Shugaban Mozambique ya nemi tallafin makwafta game da magance ta'addanci

Karon farko shugaban kasar Mozambique ya yi bayani game da halin da arewacin kasar ke ciki na karuwar hare-haren masu ikirarin jihadi.

 Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi.
Shugaban kasar Mozambique Filipe Nyusi. LUSA - MIGUEL A. LOPES
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da ‘yan ta’addda suka kaddamar da wani kazamin hari a garin Macomia cikin daren Juma’ar da ta gabata.

Yayin da yake jawabi a gidan talabijin, shugaban kasar Filipe Nyusi ya ce  garin da ke birnin Cabo Delgado na cikin yankunan dake da albarkar iskar Gas, kuma an jima ana jin kishin-kishin din mayakan IS a wajen, tun bayan da suka kaddamar da harin farko a 2017 a kasar.

Duk da yadda kasar ke cigaba da tsaurara matakan tsaro, amma dai ayyukan ta’addanci na karuwa tun watan Janairun bana.

Wasu majiyoyin jami’an tsaro da suka bukaci a sakaya sunan su sun shaidawa manema labarai cewa bincike ya tabbatar da cewa akwai daruruwan mayakan na IS   a wannan gari.

Yayin bayanin sa da safiyar yau, shugaba Nyusi yace har zuwa safiyar yau Lahadi wannan gari na ci gaba da fuskantar hari, da kuma musayar harbin bindiga tsakanin ‘yan ta’adda da kuma jami’an tsaro.

Harin na ranar Juma’a shine mafi muni da kasar ta taba gani

Shubagan ya bukaci kasashe makwafta da su taimaka wajen wajen ganin ayyukan ta’addancin basu mamaye kasar ba, kiran da tuni Rwanda ta amsa ta hanyar aikewa da dakaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.