Tsananin sanyi da dusar kankara na cigaba da addabar sassan Amurka
Tsananin sanyi da saukar dusar kankara na cigaba da addabar wasu yankunan kasar Amurka, inda zuwa yanzu rahotanni suka ce, adadin wadanda suka mutu a dalilin iftila’in ya kai mutane 32.
Wallafawa ranar:
Bayanai daga garin Buffalo da ke yammacin birnin New York na cewa akwai fargabar adadin mamatan ka iya karuwa, sakamakon yadda saukar dusar kankarar ya rutsa da mutane da dama da a yanzu suke makale a cikin motocinsu.
Tun a ranar Juma’ar da ta gabata mahukuntan New York suka haramtawa mazauna yankin Erie da ke yammacin birnin zirga-zirga da motoci, amma duk da haka daruruwan mutane suka makale a cikin ababen hawan nasu tun daga karshen mako a yayin da ake bikin ranar Kirsimati.
Guguwar dusar kankarar da ke ratsa gabashin Amurka ta katse wutar lantarkin mutane kusan miliyan 2 a tsakanin jihohin Maine da Seattle.
Sai dai daga bisani mahukuntan yankunan sun bayyana samun nasarar maidawa mutane fiye da miliyan 1.5 lantarkin da suka rasa, nasarar da ko shakkaha babu za ta ceto rayukan dubban mutanen da a bayan suka fada hatsarin rasa rayukansu, a dalilin rashin nau’rorin dumama dakunansu, wadanda ke amfani da wutar lantarki.
Guguwar dusar kankarar da ta mamaye yankunan Amurka da dama dai ita ce mafi muni da aka gani a cikin gwammman shekaru na tarihin kasar, inda ta tilasa soke tashin jiragen sama kusan dubu 12 a tsakanin Juma’a zuwa ranar Lahadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu