Isa ga babban shafi

Shugaban Amruka Joe Biden da na Majalisar Wakilai, Kevin McCarthy sun fara fahimtar juna.

shugaban Amruka Joe Biden da shugaban Majalisar wakilai Kevin McCarthy sun sake yin wani zama a fadar shugabancin Amruka dake washington a marcen jiya litanin, a yayin da lokaci ke kurewa wajen cimma yarjejeniya kan matsayin bashin kasar.

shugaban Amurka  Joe Biden ya tattauna da shugaban majalisar wakilai, Kevin McCarthy,
shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna da shugaban majalisar wakilai, Kevin McCarthy, AP - J. Scott Applewhite
Talla

A lokacin tattaunawar, M. McCarthy ya furta wasu kalamai masu karfafa guiwa kan fahimtar juna  a tsakaninsu.  sai dai babu wata yarjejeniyar da aka cimma, sun  dai tattaunawa ne kan komai a cewar M. McCarthy, lokacin da aka yi masa tambaye shi kan matsa kaimi a fannin tallafin jinkai da abinci, ya ce har yanzu maganar tana kan tebur

M. McCarthy ya ci gaba da cewa,  ya na fatan za su kai ga cimma matsayar da za ta baiwa yan majalisun  jam’iyun Républicains da Démocrate damar kada kuri’a a kai.  Haka kuma ya ce,  tattaunawar ta yi armashi sosai fiye da wace ta gabata

Bugu da karin M. McCarthy ya ce, sun yi tattaunawa ta fahimta, dangane da sabanin dake tsakaninsu da kuma ra’ayoyin da suke son aiwatarwa, lamarin da ya danganta da ci gaba mai armashi

A cikin wata sanarwa shugaban na Amruka Joe  Biden ya fitar,  shi ma ya bayyana tattaunawar a matsayin ta ci gaba da ta yi armashi sosai, inda ya ce,  da shi da shugaban majalisar wakilan sun amince, su samar da mafita ga matsalar kasa biyan bashin, dake da nasaba da  kokarin rage gibin kudaden shigar da kasa ke fuskanta.

Haka kuma shugaban ya bayyana cewa,  kamata ya yi majalisar wakilan kasar ta karkata wajen kaucewa karin haraji.

Shugaban majalisar wakilan kasar ta Amurka  M. McCarthy ya kuma  bayyana cewa, kamata ya yi majalisar wakilan, ta karkata wajen kaucewa karin haraji.

Yanzu haka  dai duk da sabanin da mazajen biyu ke da shi, amma sun amince cewa, matsalar bashin Amurka na da muhimmanci sosai a garesu.

M Biden ya ce suna da kwarin guiwar za a samu ci gaba a tattaunawar nan bada jimawa ba.

Bayan fitowarsa daga  tattaunawar M. McCarthy ya sanar da taron manema labarai cewa, babu wani yinkurin karin  kudaden bashi ga kasar Amurka, duk da cewa babu wata yarjejeniyar karshen lokaci da aka cimma  a kan haka.

A lokacin da yake yi wa yan jaridar  Capitole tsokaci  M. McCarthy  ya ce, "ya kamata a sani. Ba za mu taba gabatar da shawarar karin kudaden bashi ga Amruka a kan tebur ba. Haka kuma a majalisar dattawa ba za su taba amincewa da matakin kara daga yawan bashin ba.

Saboda haka mi ya sa zamu ci gaba da bata lokaci  kan abinda ba zai taba wucewa ba,  mai maikon mu nemi mafita ga matsalar? Mun kusa kaiwa ga manufar sosai domin sadaukar da kawunanmu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.