Isa ga babban shafi
Japan

Kasar Japon cikon shekaru 65 da harin Hiroshima

A yau an gudanar da ranar alhini ta cikon shekaru 65 da aka kai hari a garin Hiroshima na kasar Japon .Wanan hari an kai shi ne a lokacin yakin duniya na 2.Tun dai wanan lokaci shekaru 65 kenan ,a karon farko kasar Amurika ta tura wani manzo na massanman a wurin gudanar da taron .A lokacin da aka kai wanan hari ,a shekara ta 1945 ,mutane sama da dubu 140 ne suka mutu.Harin da ya yi sanadiyar mika wuyen kasar Japon ga Amurika,bayan jefa wata bomb a garin Nagazaki.Wanan kuma shine ya kawo karshen yakin duniya na 2 a shekara ta 1945.A wurin bikin nuna alhinin na yau ,da babban magatakar na majalasar dumkin duniya Ban Ki Moon ya halarta ,an yi shiru na yan mintoci domin darata rayukan margayen da su ka rigaimu sanadiyar wanan boma-bomai da aka jifa a garin Hiroshima da na Nagazaki. 

John Roos jakadan kasar Amurika a japon ataron juyayi a Hiroshima
John Roos jakadan kasar Amurika a japon ataron juyayi a Hiroshima
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.