Isa ga babban shafi
China

A kalla mutane 8 sun mutu sanadiyar gobara a Shanghai

A yau litinin a kalla mutane takwas ne suka mutu sanadiyar gobarar wuta da ta kama wani bene mafi girma a birnin Shanghai na kasar China, inda mazauna kusa da benen suka shiga rudani sanadiyar bakin hayaki da ya turmuke garin. Ginin Benen mai hawa 28 da ake wa kwaskwarima yana a unguwar da ke cunkushe da jama’a ne da mutane kusan miliyan 20 ke zama. Wata da ta samu tsira daga benen Li Xiunyun, ta bayyana cewa suna neman yadda zasu tsira da ita da mijinta da ‘ya’yanta a gidansu da ke a hawa na 16 ne suka ci karo da jami’an ceto masu kashe wuta wadanda suka taimaka wajen fitar da su a cikin benen.A yanzu haka an bayyana cewa mutane sama da 55 ne ke kwance a gadon asibiti, inda tara daga cikinsu ke cikin mayuwacin hali. 

Bakin hayakin gobarar wuta da ta tashi a bene mafi girma a Shanghai
Bakin hayakin gobarar wuta da ta tashi a bene mafi girma a Shanghai
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.