Gwamnatin Syria zata baiwa Talakawa Kudade
Hukumomi a kasar Syria sun sanar da bada tallafin kudade da suka kai Dalan Amirka miliyan 250 ga marasa karfi kimanin 420,000 dake kasar.Ministan Kula da jin dadin jama'a da Kodago na kasar Diala Haj-Aref ya fadawa manema labarai yau cewa matakin na daga cikin matakan da Gwamnatin kasar ta dauka domin ganin an taimakawa magidanta su kasance sun sami abin hannun su.Tallafin inji Ministan sun hada da rancen kudade daga watan gobe.Kamar yadda Fira Ministan kasar mai kulada harkokin tattalin arzikin, Abdallah Dardari ke cewa kashi 14% na alummar kasar miliyan 22 suna fama da talauci.Gwamnatin kasar Syrian ta kuma bayyana cewa zata sarrafa wasu kudade da suka kai Dolan Amirka biliyan 14 wajen wasu ayyukan cigada nan da shekaru biyar.
Wallafawa ranar: