Isa ga babban shafi
Siriya

Babbar Zanga-zanga yau a kasar Siriya

A kasar Siriya yau dubban jama’a suka fito a cikin tituna na birnin Damascus domin ci gaba da gudanar da zanga-zangar nuna kyamar Gwamnatin kasar, da Shugaba Bashar Al-Assad ke jagorenta.An yi gangarumar zanga-zanga a biranen Daraa, Qamishli da kuma Hasakah.Kafofin watsa labarai sun fadi cewa, jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki maisa kwalla domin tarwatsa gangamin da a ka yi a birnin Damascus.Cikin wata sanarwa ta farko tun fara zanga-zangan da ta doki tsawon makonni 5 da suka gabata, gamayyar kungiyoyin dake shirya gangamin tare da gudanar da zanga-zanga sun ce suna bukatar sauyi cikin lumana, kamar yadda taken fafutukansu yake nunawa. 

Masu zanga-zangar Syria
Masu zanga-zangar Syria
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.