Japan
Japon na son kawo karshen takunkumin fitar da kayenta a waje
Ministan harkokin wajen kasar Japan Takeaki Matsumoto ya nemi kawo karshen takunkumin fitar da kayan abincin kasar zuwa kasashen duniya, wanda aka kargamama kasar bayan girgizar kasa da igiyan ruwan Tsunami su ka janyo matsalr yoyon nukiliya.Ministan ya bayyana haka a birnin London na kasar Birtaniya yayin ganawa da takwaransa William Hague. Matsumoto ya ce, Japan ta kawar da duk wani fargabar kasashen duniya bisa matakan data dauka.
Wallafawa ranar: