Isa ga babban shafi
Siriya

Dakarun Siriya sun tsallaka cikin Turkiya

Dakarun sojan kasar Siriya, sun nausa kusa da kan iyakar kasar da Turkiya, yayin da gwamnati ke neman hanyoyi dakile zanga zangar kan kaddamar da sauye sauyen siyasa.Dubban ‘yan Siriya sun tsallaka sansanonin ‘yan gudun hijira na Turkiya, domin kaucewa matakin soja cikin yankuna na Arewacin kasar.Masu raji neman tabbatar da demokaradiya sun zargi dakarun Siriya da kutsa kai cikin kasar Turkiya, inda ake da fiye da ‘yan gudun hijira 10,000 tuni Amurka ta gargadi mahukuntan Siriya kan abunda zasu iya fuskanta idan suka ci gaba da kunnen uwar shegu bisa matakin da suke dauka.Jiya Jumma’a an hallaka masu zanga zanga 19, yayin artabu da jami'an tsaron kasar ta Siriya. Tuni Shugaba Bashar al-Assad na Siriya ke kara samun matsin lamba na kasashen duniya, domin ya sassauta matakan da dakarun kasar ke dauka. 

Masu zanga-zanga na kasar Siriya
Masu zanga-zanga na kasar Siriya Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.