Isa ga babban shafi
siriya

Siriya ta yi kashedi game da katsalanda da ake mata a cikin lamurenta

Gwamnatin kasar Siriya ta yi watsi da duk wani yunkurin shiga cikin rikicin kasar daga kasashen ketere.Ta kuma suki matakin Tarayyar Turai na tsawaita takunkumin da ta saka ma kasar.Ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem ya shaida ma tashar gidan talabijin ta kasar cewa: kowa ya ji da abunda ke damunshi ,wanan Magana na nuni ne na katsalandan da kasar Faransa ke yi ma sauran kasashen duniya a cikin lamuren sun a yau da kullin. Ranar 23 ga watan Mayu kungiyar Tarayyar Turai ta kargama takunkumi ga Shugaba Bashar al-Assad na kasar ta Siriya, game da matakan da ya doka na dakile masu zanga-zanga da karfi da gwamnatin kasar ke dauka.Babban jami’in Majalasar Dumkin Duniya Ban Ki-moon ya nemi mahukuntan kasar ta Siriya da su amince da masu bincike na kasa da kasa, tare da masu bayar da kayan agaji zuwa cikin kasar, inda aka kwashe tsawon watanni ana zanga-zangar neman sauye -sauyen demokaradiya.Ban Ki-moon ya ce shugaba Assad ya rasa kimarsa na ci gaba da jagoranci, tare da neman kawo karshen rarrabuwa a majalisar kasar. 

Shugaban Siriya Bashar el-Assad jawabi kan ricikin kasar
Shugaban Siriya Bashar el-Assad jawabi kan ricikin kasar REUTERS/Sana/Handout
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.