Libya
Shugaban Libya Gaddafi ya yi watsi da amincewa da 'yan tawaye da kasashen Yamma suka yi
Shugaban Libya Muammar Gaddafi ya yi watsi da amincewar da manyan kasashen duniya dukayi na daukan majalisar wucin gadi ta ‘yan tawaye, a matsayin wakilan al’umar kasar.A cikin wani jawabi da aka yadata kafofin yada labarai na kasar, shugaba Gaddafi, ya shaida wa dubban magoya bayansa a garin Zlitan, ya ce wannan ba komai bane, kuma babu jada baya.Ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun ‘yan tawayen dana shugaba Gaddafi, yayin da hanyoyin siyasa suka cije.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: