Isa ga babban shafi
Labanon

An fitar da sunayen wadanda ake zargin su da kashe Mr Harairi

Kotun musamman ta MDD ta byyana wallafa sunayen wadanda ake zargi da hallaka tsohon PM kasar Lebanon Rafik Hariri cikin shekara ta 2005. Maigabatar da kara na kotun Daniel Bellemare yayi maraba da matakin wanda yace zai kai ga shariyar yan Hezbollah 4 da ake zargi da hanu wajen kisan.Alkalin Kotun Daniel Fransen ya nemi kawo karshen killace sunayen wadanda ake zargi, Salim Ayyash mai shekaru 47, Mustapha Baddreddine mai shekaru 50, Hussein Anaissi dan shekaru 37 da Assad Sabra mai shekaru 34. Saboda gwamnatin Lebnon ta kasa cafko wadanda ake zargin.An kafa kotun ta musamman ta Majalisar Dinkin Duniya MDD, bayan hari da aka kai da bama bamai kan tawogar motocin tsohon Prime Ministan kasar ta Lebanon Rafik Hariri ranar 14 ga watan Febrairun shekara ta 2005, yayi sandiyar hallaka Hariri da sauran mutane 22 gami da dan kunar bakin waken day a kai harin, kuma wannan umurni zai janyo a ci gaba da gudanar da shari’ar.Kungiyar Hezbollah ta sha musanta hanu wajen kisan Mr Hariri.  

Rafik Hariri
Rafik Hariri
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.