Afghanistan
Tsohon Shugaban Afganistan Rabbani ya mutu
Jami’an tsaro a kasar Afganistan sun tabbtar da mutuwar tsohon shugaban kasar Burhanuddin Rabbani wanda ya jagoranci tattaunawar neman zaman lafiya, a wani harin kunar bakin wake da aka kai masa gidansa a Kabul.Rabbani shi ne jagoran Majalisar shugaba Hamid Karzai ta neman zaman lafiya wadda aka daurawa alhakin sasantawa da kungiyar Taliban.Harin dai ya faru ne kusa da Ofishin Kekadancin Amurka a Kabul, kuma wannan shi ne hari na biyu cikin mako daya da ake kaiwa a birnin Kabul yankin ofishin jekadancin kasashen waje.
Wallafawa ranar: