Isa ga babban shafi
EU-Syria

Kasashen yammaci sun janye matakin kakubawa Syria takunkumi

Kasashen Yammacin Duniya, sun janye bukatar su na kakubawa Gwamnatin Syria takunkumi a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dunkin Duniya, saboda shirin kasashen Russia da China na hawa kujerar na-ki akai.Wani sabon daftari da kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Portugal suka rubuta, da goyan bayan Amurka, ya bayyana dakatar da shirin, sai dai kuma kasashen sun yi barazanar daukar mataki muddin aka ci gaba da samun zubar da jini a cikin kasar.Daga cikin kasashen da suka bayyana adawa da matakin kakubawa kasar Syria Takunkumi sun hada da kasar Indiya da Africa ta kudu da Brazil 

Shugaban kasar Syria Bashar Assad.
Shugaban kasar Syria Bashar Assad. (REUTERS)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.