Isa ga babban shafi
Amurk-Isra'ila

Amurka ta gargadi Isra’ila akan matsayinta a Gabas Ta Tsakiya

Kasar Amurka ta gargadi Isra’ila cewar, karfin sojin da take gadara da shi, ba zai iya magance mata matsalar diplomasiyar da take fuskanta da makwabtanta ba.Sakataren Tsaron Amurka, Leon Panetta ne ya yi wannan gargadi yayin da ya kai ziyarar aiki a Isra’ila, inda yake cewa, ya zama wajibi ga kasar ta sasanta da makwabtanta da ke Yankin, musamman kawayen ta.Mista Panetta yace, karfin soji ba zai taimake ta ba, muddin ta kasa sasantawa da makwabtanta domin samun zaman lafiya, musamman a halin yanzu da aka samu juyin juya hali a wasu kasashen dake Gabas ta Tsakiya.Sakataren yace zasu yi iya bakin kokarinsu wajen sasanta Isra’ila da kasashen Masar da Turkiya, domin kin amincewa da haka, ba zai taimaki kasar ba.Ana saran Panetta zai gana da shugabanin Isra’ila da Palasdinu, kafin ya kai ziyara Masar da kuma taron kungiyar NATO. 

Leon Panetta tare da Sakatariyar Harakokin wajen Amurka Hillary Clinton
Leon Panetta tare da Sakatariyar Harakokin wajen Amurka Hillary Clinton (AFP)
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.