Isa ga babban shafi
Turkiya

Dakarun Turkiya na mayar da martani kan kisan mutane 26

Yanzu haka kurar ya ki ta turnike tsakanin dakarun kasar Turkiya da na kungiyar yan tawayen PKK ta Kurdawa yankunan kan iyakar kasar da Iraki sakamakon kashe dakarun gwamnatin Turkiya 26 da yan tawayen kudawan suka yi.Majiyar tsaron gwamnatin Turkiya a yankin kan iyakar ta bayyana cewa dakarun jam’iyar ma’aikatan ta Kurdawa PKK, ba tare da Kakkautawa ba sun kai hare hare a kan zanguna takwas, a garuruwan Cukurka da Yuksekoya, dake cikin yankin Hakkari dab da kan iyakar kasar da kasar Iraki inda suka kashe jami’an tsaron Turkiya 26.Wannan ya haifar da mayar da Martani daga dakarun Gwamnati da munanan luguden wutar soja ta sama da kasa, akan 'yan tawayen na PKK a Tsaunukan kan ikar Turkiya da Iraki.Rahotanni sun bayyana cewa sama da dakarun gwamnati ta Turkiya 1000 ne, yanzu haka suka yi wa 'yan tawayen kawanya, domin hanasu kaiwa ga maboyarsu ta karshe.Kakakin kungiyar PKK Dozdar Hammo ya shaidawa AFP cewa, dakarun Turkiya sun kutsa kai a cikin kasar Iraki ta yankin Hakkari, amma gwamnati Iraki ta ce babu tabbaci kan labarin.Yanzu haka dai jiragen saman kasar Turkiya na ci gaba da yiwa 'yan tawayen na PKK Ruwan wuta a yankin arewacin kan iyakar kasar da Iraki, wanda ya hada da garin Qandil, tingar karshe ta yan tawayen na PKK. 

AFP / SAFIN HAMED
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.