Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta dauki taro kan zaman Lafiya cikin kasashen Asiya

A yau Laraba ne, birnin Istambul na kasar Turkiya ya karbi bakuncin zaman taron kasashen duniya, kan karfafa wanzuwar zaman lafiya a yankin Asiya musaman a kasar Afghanistan da yaki ya daidaita.Kasashen duniya sama da 20, tare da wasu kungiyoyin duniya ne, suka halarci zaman taron na yau a birnin Istambul na kasar ta Turkiya, a kokarin da ake na samar da zaman lafiya a yankin Asiya, a karkashin jagorancin kasashen Turkiya da Afghanistan.Zaman taron na wuni guda da ya samu halartar Ministocin harakokin wajen kasashen Faransa Alain Juppe, da na kasar Jamus Guido Westerwelle zai fitar da sanarwar bai daya kan samar da zaman lafiya a yankin na Asiya.A lokacin da yake jawabi a wajen taron shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai, ya nemi kasashen duniya da su kara taimakawa wajen magance matsalar yakin da ya daidaita kasarsa, inda ya ce mawuyacin abu ne a samu zaman lafiya matsawar ba kawo karshen aiyukan ta’addanci a kasar ta Afghanistan ba.Karzai ya kara da cewa ta’addanci ya samu gidin zama a kasar Afghanistan dan haka sai kasashen yankin na Asiya sun bada gagarumar gudummawa wajen magance shi, matsawar ba haka ba kuwa babu yadda za’a samu zaman lafiya a yankin na Asiya. 

Daga hanun hagu zuwa dama, Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan da Abdullah Gul na Turkey da Asif Ali Zardari na Pakistan
Daga hanun hagu zuwa dama, Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan da Abdullah Gul na Turkey da Asif Ali Zardari na Pakistan Reuters/Murad Sezer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.