Isa ga babban shafi
Afganistan

Yunkurin sasantawa da Taliban a Afganistan ya ci tura

Tsohon Ministan harakokin wajen kasar Afghanistan Mohammad Haneef Atmar yace duk wani kokarin da ake yi na hawa teburin sasantawa da kungiyar Taliban ya ci tura.Mohammad Haneef wanda ke jawabi yayin wata lakca a kasar Amurka ya ce wadanda suka ajiye makamai ya zuwa yanzu ba su ne babbar barazanar kasar ba.A ranar 20 ga watan Satumba ne wani dan kunar bakin wake, ya tayar da bom din da ya hallaka tsohon shugaban kasar ta Afghanistan Burhanuddin Rabbani, da gwamnatin Karzai ta dora wa alhakin neman sasantawa da ‘Yan kungiyar ta Taliban. 

Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.